Wata Kotun Koli a kasar Sin ta zartar da hukuncin kisa ga wani mutum da ya yi tukin ganganci, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 35 tare da jikkata 43 a birnin Zhuhai da ke kudancin kasar a watan Nuwamba.
Hakan na kunshe ne acikin wani rahoto da gidan talabijin na kasar Sin, CCTV ya fitar a ranar Litinin, 20 ga watan Janairun 2025.
- Bidiyon Rashin Ɗa’a: Hukumar Tace Fina-finai Ta Dakatar Da Soja-boy Daga Shiga Duk Wata Harka Ta Kannywood
- Kafar CMG Ta Nuna Sassan Kirkire-kirkire Da Za A Yi Amfani Da Su Yayin Bikin Murnar Sabuwar Shekarar Gargajiya Ta Sin Ta Bana
A cewar kotun “A ranar 11 ga Nuwamba, Fan Weiqiu mai shekaru 62 da gangan ya tuka wata karamar mota kirar SUV ta cikin taron jama’a, inda hakan ya yi sanadin mutuwar mutane 35 tare da raunata 43. Wannan shi ne hari mafi muni da ya afku a kasar tun 2014.”
An yanke masa hukuncin kisa a watan da ya gabata, inda kotun ta ce, dalilansa “sun wuce gona da iri, laifin ya yi muni da yawa, wannan ya haifar da babbar illa ga al’umma”.
CCTV ta fada a ranar Litinin cewa, mai gabatar da kara na Zhuhai “ya aika da jami’ai don sa ido kan aiwatar da hukuncin bisa ga doka.”
Kotun ta gano cewa, wanda aka yanke wa wannan hukuncin, “ya yanke shawarar yin tukin ganganci ne don huce fushinsa, biyo bayan mutuwar aurensa da takaicin rashin gamsuwa da raba dukiyarsa.”