Hukumar kula da binciken sararin samaniyar kasar Sin (CNSA) ta bayyana yawan na’urorin nazarin kimiyya da kasashen duniya za su ajiye, wajen gudanar da aikin binciken duniyar wata na Chang’e-6 tare da sanar da wani kira ga kasa da kasa, na shawarar ajiye na’urorin game da shirin binciken na Chang’e-7.
Hukumar ta sanar da cewa, za ta dauki na’urorin kimiyya daga kasashen Faransa da Italiya da hukumar kula da sararin samaniya ta Turai/Sweden a na’urar Chang’e-6 da kuma wani nau’ na kayan aikin Pakista a kan na’urar da za a harba. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp