Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta ce, a ranar 19 ga wannan wata, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya yi bayani game da yanayin tafiyar tattalin arzikin kasar Sin a watan Afrilu, inda kafofin watsa labaru na kasa da kasa suka yi amfani da kalmomi kamar “wuce zaton da aka yi” da kuma “ da karfi” wajen yabawa tattalin arzikin kasar Sin.
Mao Ning ta bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Laraba, inda ta ce, bisa yanayin tinkarar harajin kwastam mai yawa, kasar Sin ta tabbatar da bunkasar cinikayyar kasa da kasa.
A farkon watanni 4 na bana, yawan kudin kayayyakin shige da fice na kasar Sin ya karu da kashi 2.4 cikin dari, a cikinsu yawan kudin kayayyakin da aka fitar ya karu da kashi 7.5 cikin dari, lamarin da ya shaida cewa, Sin tana da karfin yin takara a duniya. Haka zalika, Sin ta kara bude kofa ga kasashen waje, da sa kaimi ga kamfanonin kasashen waje da su kara samun ci gaba da wuce zaton da aka yi a kasar. Wadannan duka sun shaida cewa, Sin tana da karfi wajen tinkarar hadari da kalubale a fannoni daban daban. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp