• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Tana Dora Muhimmanci Kan Dangantakar Abokantaka Ta Gargajiya Da Rwanda

bySulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
Sin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning, ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum yau Talata.

Dangane da sakamakon babban zaben kasar Rwanda, Mao Ning ta ce, shugaba Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga shugaba Paul Kagame ta hanyar diplomasiyya, bisa sake zabarsa a matsayin shugaban kasar. A ko da yaushe kasar Sin tana mutunta dangantakar abokantaka ta gargajiya tsakaninta da kasar Rwanda, kuma tana son yin hadin gwiwa da kasar Rwanda wajen zurfafa mu’amala da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban.

  • Wang Yi Ya Jaddadawa Manyan Jami’an USCBC Aniyar Sin Ta Zurfafa Gyare-gyare Da Kara Bude Kofa Ga Kasashen Waje
  • Wang Yi: PLO Ita Ce Kadai Halatacciyar Wakiliyar Al’ummar Falasdinu

Dangane da taron shirya babban taron bita kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya da ke gudana a birnin Geneva, Mao Ning ta bayyana cewa, babbar manufar kasar Sin ta shiga wannan taro ita ce, ya kamata kasashe masu mallakar makaman nukiliya su mai da martani game da damuwa da bukatu na kasashen da ba su da makaman nukiliya, da kuma kulla yarjejeniya cewa ba za a zama na farkon yin amfani da makaman nukiliya kan juna ba ko fitar da wata sanarwar siyasa.

Kan tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin Falasdinu da kasar Sin ta shirya, Mao Ning ta bayyana cewa, wannan shi ne karo na farko da bangarorin Falasdinu 14 suka hallarta a nan birnin Beijing, domin gudanar da shawarwarin sulhu, wanda ya kawo kyakkyawar fata ga al’ummar Falasdinu dake cikin wahala.

Dangane da Amurka ta sayar da makamai ga yankin Taiwan, Mao Ning ta ce, lamarin ya keta manufar kasar Sin daya tak, da kuma yarjejeniyoyi guda uku da Sin da Amurka suka daddale, Sin na adawa da hakan sosai.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Game da rikicin kasar Ukraine, Mao Ning ta ce, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan zaman lafiya da tattaunawa, tare da nuna goyon baya ga al’ummomin kasa da kasa wajen samun karin fahimtar juna, da kuma neman hanyoyin da za a bi wajen warware rikicin ta hanyar siyasa. (Safiyah Ma)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Da’awar Zanga-zanga: An Sako Abusalma Daga Gidan Yari

Da'awar Zanga-zanga: An Sako Abusalma Daga Gidan Yari

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version