Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Dai Bing, ya bayyana a jiya Talata cewa, kasar Sin tana fatan bangarori daban daban na kasar Libya, za su maida hankali ga moriyar dukkanin sassan kasar, su daidaita matsalolinsu ta hanyar yin shawarwari, da sa kaimi ga samun ci gaba a yunkurin daidaita siyasar kasar.
A kwanakin baya, bangarori daban daban na kasar Libya sun yi shawarwari, tare da cimma daidaito kan zaben shugaban kasar. Game da hakan, kasar Sin ta yi kira ga sassan kasa da kasa da su saurari kiran kasar Libya da damuwarta, da girmama ikon mulkin kasa, da cikakkun yankunan kasar Libya, da kuma magance tilastawa mata amincewa da shirin daidaita matsalar kasar da kasashen waje suka gabatar. Har ila yau, Sin ta yi kira ga dakaru, da sojojin haya na kasashen waje, da su gaggauta janyewa daga kasar Libya.
Dai Bing ya kara da cewa, kwamitin kula da batun Libya na kungiyar AU, ya sa kaimi ga gudanar da taron sulhuntawa na kasar Libya. Kasar Sin ta yabawa jamhuriyyar dimokaradiyyar Congo, bisa muhimmiyar rawa da ta taka wajen daidaita matsalolin Afirka ta hanyar tsarin Afirka. Tana kuma fatan kasashen nahiyar za su gaggauta gudanar da taro, kana bangarori daban daban na kasar Libya za su rungumi taron a matsayin damar sa kaimi ga samun zaman lafiya da sulhuntawa, da hada kai da cimma ra’ayi daya, don taimakawa kasar Libya canza shugabanci, da samun bunkasuwa mai dorewa yadda ya kamata. (Zainab Zhang)