• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Tana Kawo Tabbaci Ga Duniya Yayin Da Take Cikin Yanayi Na Tangal-Tangal

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Yanzu haka kasashen duniya suna cikin yanayi mai sarkakiya, kuma ba a kai ga shawo kan annobar cutar COVID-19 ba tukuna, kana tattalin arzikin duniya yana kara fuskantar koma baya, baya ga matsalar karancin makamashi da hatsi sakamakon tsananta rikicin Ukraine.

A hannu guda kuma tunanin yakin cacar baki, da siyasar nuna fin karfi, da ra’ayin bangaranci da kare moriyar kashin kai, sun sake bulla a fadin duniya.

  • Adadin Kudin Shigar Kayayyakin Manhajar Masana’antun Sin A Watanni 7 Na Farkon Bana Ya Karu Da Kaso 8.7 Bisa Dari

A game da wannan batu, a jawabin da ya gabatar yayin taron muhawara na babban taron MDD karo na 77, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya sake yin bayani kan shawarwarin tabbatar da tsaron duniya da raya duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, inda ya zayyana manufofi shida, wadanda suke tabbatar da wanzar da zaman lafiya a maimakon rikici, da raya kasa a maimakon talauci, da bude kofa ga ketare a maimakon rufe kofa, da gudanar da hadin gwiwa a maimakon nuna kiyayya, da hada kai a maimakon kawo baraka, da tabbatar da adalci a maimakon nuna fin karfi, manufofin dake nuna matsayin kasar Sin game da muhimman batutuwan da suka shafi harkokin kasa da kasa.

Shugaban babban taron MDD karo na 77 Korosi Csaba, ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa, kuma muhimman shawarwarin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, su ma sun samar da dabarun daidaita kalubalolin da kasashen duniya ke fuskanta a halin da ake ciki yanzu.

Shi ma babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yaba wa muhimmiyar rawar da kasar Sin da dade tana takawa, wajen goyon bayan manufar tafiyar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, da ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, da samun dauwamammen ci gaba da sauransu.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Yana mai bayyana cewa, MDD tana goyon bayan shawarar raya kasashen duniya baki daya da shugaba Xi ya gabatar, yana mai cike da imani cewa, shawarar za ta taimakawa yunkurin samun dauwamammen ci gaban duniya nan da shekarar 2030.

Duk da cewa, kalulabe da kasashen duniya suke fuskanta, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawar da ta dace don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa
Daga Birnin Sin

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Next Post
Tsohon Kaftin Din Super Eagles, Mikel Obi Ya Yi Ritaya Daga Buga Kwallon Kafa

Tsohon Kaftin Din Super Eagles, Mikel Obi Ya Yi Ritaya Daga Buga Kwallon Kafa

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025

October 25, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025

Gwamnatin Katsina Ta Ƙara Samar Da Dakarun Tsaro 200 Domin Maganace Ta’addanci

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.