An gudanar da taron kwamitin gudanarwa na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya, wato IAEA a takaice na watan Yuni a Vienna, fadar mulkin kasar Austria a ranar 3 ga wata. Mataimakin darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar Sin Liu Jing, ya halarci taron tare da gabatar da jawabi, inda ya yi karin haske kan matsayin kasar Sin a dukkan fannoni. Kaza lika ya bayyana fatansa na amfani da damammakin cika shekaru 40 da shigar kasar Sin cikin hukumar IAEA, wajen hada hannu da hukumar kan tabbatar da shawarar raya kasa da kasa da shawarar tsaron kasa da kasa.
A cikin jawabinsa, Liu Jing ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan muhimmiyar rawar da makamashin nukiliya ke takawa wajen samar da ci gaba mai dorewa a duniya, kana tana tsayawa tsayin daka kan raya makamashin nukiliya cikin tsaro kuma bisa tsari, da kuma amfani da makamashin nukiliya a matsayin muhimmin zabi don kafa sabon tsarin makamashi da cimma burin kaiwa kololuwar fitar da hayakin Carbon zuwa shekarar 2030, da kuma kawar da illarsa zuwa shekarar 2060.
- Sanata Yari Ya Samar Da Taki Ga Manoman Zamfara A Kan Naira 20,000
- Sin Na Fatan EU Za Ta Kiyaye Cinikayya Cikin ‘Yanci Tare Da Yin Watsi Da Ba Da Kariya
Liu Jing ya bayyana cewa, kasar Sin na kara karfafa yin amfani da fasahar nukiliya don raya aikin gona, kuma karfin masana’antar likitanci dake amfani da nukiliya yana kara samun ci gaba cikin sauri. Baya ga haka, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan batutuwan da suka shafi tsaron nukiliya, da inganta yanayin aiki da ingancin gina tashoshin nukiliya, da ma inganta matakan tsaro na cibiyoyin nukiliya da kayayyakin nukiliya, da kuma kara karfin yaki da ta’addanci mai nasaba da nukiliya.
Dangane da batun kwarara ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku da kasar Japan ke yi, Liu Jing ya jaddada cewa, kamata ya yi hukumar IAEA ta kafa ingantaccen tsarin sa ido na kasa da kasa mai zaman kansa na dogon lokaci, domin tabbatar da irin ayyukan da kasar Japan ke yi, ba zai kawo illa na dogon lokaci ga yanayin ruwa da lafiyar dan adam ba. (Bilkisu Xin)