Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce fashewar da ta lalata bututun iskar gas na Nord Stream, wanda babban muhimmin aiki ne na jigilar iskar gas, na da mummunan tasiri ga kasuwar makamashi ta duniya, da muhallin halittu, kuma hakan zai sanya kasashen duniya cikin damuwa, game da tsaron manyan ababen more rayuwa da ake da su.
Wang Wenbin, wanda ya bayyana hakan a Alhamis din nan, ya kara da cewa, ya zama wajibi a gudanar da bincike bisa adalci, da kwarewa, tare da hukunta wadanda suke da hannu cikin aikata wannan ta’asa. (Saminu Alhassan)