Mataimakin shugaban hukumar tsara manufofin ci gaba da sauye-sauye a kasar Sin Zhao Chenxin, ya ce kasar za ta fitar da tsare-tsaren da za su taimaka wajen daidaita samar da guraben ayyukan yi, da bunkasa tattalin arziki tare da ingiza ci gaba mai inganci.
Zhao, wanda ya shaida hakan yayin taron manema labarai na Litinin din nan, ya ce za a aiwatar da sabbin tsare-tsaren a sassa 5, da suka hada da karfafa sashen samar da guraben ayyukan yi, da wanzar da daidaito a fannin cinikayyar waje, da yaukaka sayayya, da fadada zuba jari, da kara inganta yanayin samar da ci gaba.
Ya ce, a fannin samar da guraben ayyukan yi, gwamnatin Sin za ta karfafa gwiwar mamallaka sana’o’in wajen daidaita matsayin guraben aiki, da karfafa samun horo na kwarewar fasahohi, da fadada shirye-shiryen rage nauyin ayyuka, da karfafa tasirin hidimomi da ake samarwa ga jama’a.
Kazalika, domin daidaita ci gaban cinikayyar waje, manufofin da za a aiwatar sun hada da na tallafawa kamfanonin dake fitar da hajoji, ta yadda za su rage hadurra daka iya aukuwa, da fadada fitar da hidimomin da ake samarwa ga karin sassan duniya, da karfafa gwiwar kamfanonin waje, ta yadda za su kara zuba jarinsu a kasar ta Sin.
Daga nan sai jami’in ya bayyana cewa, Sin na da isassun manufofi da tsare-tsare, da za su wanzar da burinta na raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma a shekarar nan ta bana. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp