Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin a ranar Alhamis ta ce za ta kaddamar da bincike a kan abubuwan hada laturoni na ‘semiconductors’ masu rahusa da Amurka take fitarwa zuwa kasashen waje.
Da yake bayar da amsa game da tambayar da aka yi dangane da tasirin shigo da abubuwan hada laturonin masu rahusa daga Amurka zuwa masana’antun kasar Sin, mai magana da yawun ma’aikatar ya ce, tabbas ana nuna damuwa a wannan sashen dangane da tallafin da gwamnatin Biden take bayarwa ga masana’antun kera abubuwan hada laturoni na ‘semiconductor’. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)