Manazarta na kasa da kasa sun yi imanin cewa, a kwanan baya kasar Sin ta dauki matakan da suka dace don ba da cikakken goyon baya ga raya wasu sassan tattalin arziki, a kokarin kara azama kan bunkasar tattalin arzikin kasar. Kana wani jami’in bankin Standard Chartered ya ce, duk da kalubalen da ake fuskanta, har yanzu ana ci gaba da ganin yadda kasar Sin take ci gaba da bude kofar ga kasashen waje.
Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, tattalin arzikin Sin yana da karfin juriya da kyakkyawar makoma, kuma yanayin bunkasuwar tattalin arzikin kasar mai kyau na dogon lokaci bai sauya ba, Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya, da samar da karin damammaki ga bunkasuwar dukkan kasashe. (Zainab)