Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta bayyana yau Litinin cewa, kasar ta na ganin batun sake tsara fasalin basussukan Zambiya, na bukatar fahimta gami da amincewar juna tsakanin bangarori masu ruwa da tsaki, a wani kokari na lalibo hanya mafi kyau ta daidaita matsalar.
Mao ta ce, akwai kyakkyawan zumunci tsakanin kasar Sin da kasar Zambiya. Kuma har kullum kasar Sin ta kan maida hankali sosai kan batun da ya shafi basussukan Zambiya, kana, ita ce kasa ta farko da ta dauki matakin tsawaita lokacin biyan bashi ga Zambiya, daga bisani kuma ta taimaka wajen gudanar da taruka har sau uku, a matsayin shugabar kwamitin kasashen da suka samar da basussuka ga Zambiya. Ta kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da tuntuba da kara shawarwari da Zambiya, gami da sauran wasu bangarori, domin taka rawar a-zo-a-gani wajen daidaita matsalar basussukan dake addabar Zambiya.
Mao ta ce, kididdigar da ma’aikatar kudin Zambiya ta fitar ta nuna cewa, basussukan da kasashen yammacin duniya suka samar, gami da na cibiyoyin hada-hadar kudi, sun dauki kaso 70 bisa dari na dukkan basussukan da Zambiya take ci, don haka ya zama dole su dauki nauyin kara daukar matakai masu amfani domin rage matsin lambar da Zambiya take fuskanta na biyan basussuka. (Murtala Zhang)