Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira wani taron manema labarai a yau Talata, inda darektan hukumar aiwatar da kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje Zheng Shanjie ya bayyana cewa, Sin za ta dauki jerin matakai bisa halin da ake ciki yanzu, don sa azama kan bunkasuwar tattalin arzikinta.
Ya ce, game da matsin lambar da ake fuskanta, za a kyautata harkokin tattalin arziki bisa manufofi masu ruwa da tsaki daga manyan fannoni. Kana game da matsalar karancin bukatu a cikin gida, Sin za ta dauki matakan amfanar da al’umma, da ingiza sayayya da muhimmanci, yayin da take aiwatar da manufar habaka bukatun cikin gida. Kaza lika, game da wahalhalun da wasu kamfanoni ke fuskanta, za ta kara daukar matakan ba da taimako da ma kyautata yanayin ciniki. Kuma game da batun rauni a bangaren sayen gidaje, da raguwar farashin hannun jari da dai sauransu, Sin za ta dauki matakai masu karfi.
- Muna Tattaunawa Don Ganin An Tsagaita Wuta A Yakin Gabas Ta Tsakiya – Kamala Harris
- Gwamnati Ba Za Ta Ci Gaba Da Biyan Tallafin Aikin Hajji Ba – NAHCON
Zheng ya ce, tattalin arzikin Sin na tafiya yadda ya kamata ba tare da tangarda ba, duk da yanayi mai sarkakiya da ake fuskanta a gida da waje, inda kuma ake samun sabon karfin samar da hidimomi da hajoji masu karko cikin sauri, da ma samun ingantattun bunkasuwa yadda ya kamata.
Zheng ya kara da cewa, dorewa da bunkasuwa kalmomi ne 2 masu dacewa wajen bayyana halin bunkasuwar tattalin arzikin Sin. Dorewa na nufin hakikanin ci gaba da take samu, kuma bunkasuwa na nufin tsare-tsaren dake samun kyautatuwa.
Tubalin tattalin arzikin kasar Sin bai canza ba. Ana da kwarin gwiwa wajen cimma burin bunkasar kasar Sin a wannan shekara, da ma samun dorewar bunkasuwar tattalin arziki ba tare da tangarda ba. (Amina Xu)