Wani jami’i na ma’aikatar kula da raya gidajen kwana, da birane, da kauyuka na kasar Sin, ya ce kasar za ta kara azama wajen kare kauyukan gargajiya a wurare daban-daban, da ma gaggauta shigar da sunayen wadannan kauyuka cikin tsarin al’adu mai alamar al’ummar Sinawa, da ma gudanar da aikin bincike, da kimanta kauyuka na gargajiya, da kyautata dokoki da manufofi, ta yadda za a inganta tsarin ba da tabbaci gare su.
Ma’aikatar ta kira taron ingiza ayyukan kare kauyuka na gargajiya a gundumar Wuyuan na birnin Shangrao dake lardin Jiangxi a jiya Lahadi.
An ce, ya zuwa yanzu, Sin ta shigar da sunayen kauyuka 8155 a cikin jeren sunayen kauyukan da ya kamata a kare su, tare da saka musu alamu. Ban da wannan kuma, larduna 16 sun shiga cikin sunayen kauyuka na gargajiya, a cikin jerin sunayen da ya kamata a kare su a lardunansu, inda aka ba da kariya ga gine-ginen gargajiya dubu 556, da ma gado da raya kayayyakin al’adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kaka da kakanni har 5965, matakin da ya kafa tsari mafi girma dake kare cikakkun al’adun aikin noma na gargajiya mafi daraja a duniya. (Amina Xu)