• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Za Ta Karbi Ragamar Shugabancin SCO Daga Shekarar 2024 Zuwa 2025

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
Sin

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

A yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda game da ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar Kazakhstan don halartar taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO, ta ce shugaba Xi Jinping zai yi musanyar ra’ayi mai zurfi da shugabannin kasashen dake halartar taron, don gane da zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban a karkashin sabon yanayi, da kuma manyan batutuwan duniya da na yankuna a halin da ake ciki. Jami’ar ta ce bayan taron, Sin za ta karbi ragamar shugabancin kungiyar SCO daga shekarar 2024 zuwa 2025.

Game da bikin tunawa da cika shekaru 70, da fitar da ka’idoji biyar na zaman tare cikin lumana, wanda Sin ta gudanar a baya bayan nan, Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da dukkan bangarori, wajen aiwatar da babban ra’ayin da aka cimma a yayin bikin, da sa kaimi ga ka’idoji biyar na zaman tare cikin lumana, da kuma inganta gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama.

  • Wakilin MDD Ya Bukaci Daukar Matakan Gaggawa Na Dawo Da Nijeriya Turbar Manufofin Ci Gaba Mai Dorewa (SDG)
  • Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murnar Kammalawa Da Bude Gada Kan Teku Tsakanin Shenzhen Da Zhongshan

Game da mu’amala da hadin gwiwa a bangaren nazarin sararin samaniya tsakanin Sin da Amurka, Mao Ning ta ce, kofar gwamnatin Sin a bude take a wannan fage. To sai dai kuma ga alama Amurka, ta manta da wanzuwar dokokin ta na cikin gida, irin su “Wolf Clause”, don haka babu tabbas, kan ko gwamnatin Amurka za ta ba da izinin shiga mu’amala, da hadin gwiwa tare da Sin tsakanin masana kimiyya da cibiyoyin da abun ya shafa na kasarta.

Dangane da rahoton da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, na yin kalamai marasa ma’ana kan harkokin addinai na Sin, Mao Ning ta ce, Sin ta bukaci Amurka da ta mutunta gaskiya, ta gyara kuskurenta, ta kuma daina amfani da batutuwan addini, wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Sin.(Safiyah Ma)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Next Post
An Gudanar Da Bikin Nune-Nunen Shirye-Shiryen CMG Masu Inganci A Kazakhstan Da Tajikistan

An Gudanar Da Bikin Nune-Nunen Shirye-Shiryen CMG Masu Inganci A Kazakhstan Da Tajikistan

LABARAI MASU NASABA

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

November 6, 2025
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa A Sakkwato

November 6, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025

November 6, 2025
Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025
Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.