A jiya Litinin ne dokar kare namun daji ta kasar Sin, wadda aka yiwa kwaskwarima a watan Disambar bara ta fara aiki gadan gadan, dokar da kasar ta Sin ke fatan amfani da ita wajen cimma burin kara kyautata kariya ga rayuwar namun daji da muhallan su.
Kaza lika dokar da aka yiwa gyaran fuska, na kunshe da tanadin tallafi da gwamnati ke samarwa ga wadanda suka fuskanci asara sakamakon barnar dabbobin dawa, da kuma fadada tanadin daga dabbobin dake karkashin kariyar kasa, zuwa dukkanin dabbobi masu rayuwa a doron kasa, wadanda suka haifar da mummunar illa ga bil adama.
Tun a shekarar 1988 ne aka kafa dokar baya ta kare namun daji ta kasar Sin, kana bayan yi mara gyaran fuska a karon farko a shekarar 2016, aka sake sabunta ta a watan Disambar bara. (SAMINU ALHASSAN)