Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce kasarsa za ta soke daukacin haraji kan hajojin kasashe masu karancin wadata, ciki har da kasashen Afirka 33 wadanda suka kulla huldar diflomasiyya da Sin.
Shugaba Xi, ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, cikin jawabin da ya gabatar yayin bude taron FOCAC na shekarar 2024, inda ya ce kasarsa ta shirya kara bude kasuwanninta sosai ga kasashen ketare.
Matakin a cewar shugaba Xi, shi ne irinsa na farko da wata babbar kasa mai tasowa ta aiwatar, wanda kuma zai taimaka wajen mayar da babbar kasuwar Sin muhimmiyar dama mai yalwa ga kasashen Afirka. (Saminu Alhassan)