Kasar Sin na shirin fadada tsarin sadarwar wayar salula ta 5G da na’urorin fiber mai saurin Mbps dubu 1 zuwa dukkan gundumomi da garuruwan dake kan iyakokin kasar, nan da karshen shekarar 2025.
Ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwar kasar ce ta sanar da hakan a cikin wata takardar sanarwa da ta fitar Larabar nan, tana mai cewa, tsarin na intanet zai hade dukkan kauyuka, da sassan kula da iyakoki da wuraren kasuwanci da tsibiran da ke zaune a wadannan wurare.
Sanarwar ta jaddada mahimmancin yin amfani da intanet a yankunan kan iyaka, inda ta bayyana hanyoyin sadarwar wayar hannu a matsayin “jigon samar da bayanai” don ci gaban yankunan karkara. (Mai fassara: Ibrahim)