Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce yayin da kasashe masu tasowa suka bayar da sabbin gudummawa ga sauyin tattalin arzikin duniya, da kara kyautata jagorancin duniya a shekarar 2024, kasar Sin za ta ci gaba da aiki tare da sassan kasashe masu tasowa, wajen samar da ci gaba, da ingiza nasarar zamantakewar dan adam.
Mao Ning, wadda ta bayyana hakan a jiya Talata, yayin taron manema labarai da ya gudana, ta ce a shekarar 2024, kungiyar BRICS ta gudanar da taro tare da karin sabbin mambobi, kana an gudanar da muhimman tarukan kasa da kasa, da suka hada da taron jagororin kungiyar raya tattalin arziki ta APEC karo na 31, da taro na 19 na kungiyar G20, kuma dukkaninsu kasashe masu tasowa ne suka karbi bakuncinsu, ciki har da Peru da Brazil. Har ma wasu masu fashin baki na cewa, shekarar 2024, shekara ce ta kasashe masu tasowa.
- Gwamnatin Kano Ta Yi Fatali Da Kudirin Sake Fasalin Dokar Haraji
- Gwamna Sule Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Samar Da Wutar Lantarki Mallakin Jihar Nasarawa
Da aka bukaci ta yi tsokaci game da karin tasiri da kasashe masu tasowa ke yi a harkokin duniya, Mao ta ce daukakar wadannan rukunin kasashe na tabbatar da sauyin dake wakana a duniya, kuma har kullum kasar Sin na kasancewa muhimmiyar kasa a tsakanin rukunin, ta kuma sha alwashin ingiza goyon baya, da karsashin samar da ci gaba tsakaninsu.
Bugu da kari, jami’ar ta ce Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufofi na hakika, na cimma nasarar cudanyar dukkanin sassa, da kare moriyar bai daya ta kasashe masu tasowa, da shiga a dama da ita, a yunkurin samar da nasarar goyon baya, da ci gaban kasashe masu tasowa, da ba da gudummawar ingiza nasarar ci gaban bil adama. (Saminu Alhassan)