A yau ne, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta jagoranci taron manema labarai da aka saba gudanarwa Litinin din nan. Kuma wani dan jarida ya yi mata tambaya kan tattaunawar da za a yi tsakanin manzon musamman na kasar Sin kan sauyin yanayi Xie Zhenhua da manzon musamman na shugaban kasar Amurka kan sauyin yanayi John Kerry.
Da take karin haske kan wannan batu, Mao Ning ta bayyana cewa, sauyin yanayi kalubale ne na bai daya da dukkanin bil-Adama ke fuskanta. Kamar yadda kasashen Sin da Amurka suka amince, manzon musamman na shugaban Amurka kan sauyin yanayi John Kerry zai ziyarci kasar Sin daga ranar 16 zuwa 19 ga watan Yuli, inda ake fatan za su tattauna batutuwan da suka shafi matsalar sauyin yanayi da musayar ra’ayoyi da hada hannu don fuskantar kalubale.
Haka kuma, dangane da yada zangon da wani jami’in hukumar Taiwan zai yi a Amurka a kan hanyarsa ta zuwa Paraguay a wata mai zuwa. Mao Ning ta kara da cewa, kasar Sin tana adawa da duk wani nau’i na mu’amala a hukumance tsakanin Amurka da yankin Taiwan, kuma tana adawa da hadin gwiwar Amurka da goyon bayan ‘yan aware na yankin Taiwan da ayyukansu ta kowace fuska. (Mai fassara: Ibrahim)