An yi kiyasin cewa, a lokacin hutun Bikin Bazara na bana, yawan Sinawa da za su je yawon bude ido a ketare zai kai kimanin miliyan 1.85 a kowace rana, wanda zai karu da kashi 9.5% bisa na makamancin lokacin bara, alkaluman da zai kai matsayin koli a sabon zagaye a wannan bangare.
An ce, daga ranar 28 zuwa 30 ga watan Jarairu, adadin Sinawa da za su wuce shingen kwastam zuwa ketare zai kai matsayin koli, yayin da adadin shigo da baki daga ketare shi ma zai kai koli daga ran 3 zuwa 4 ga watan Fabrairu mai zuwa.
Hukumar shige da fice ta kasar Sin ta dauki matakin da ya dace don aiwatar da ayyukanta a lokacin Bikin Bazara, inda ta bude isassun hanyoyin bincike don tabbatar da cewa, lokacin tantance masu yawon bude ido na hukumar kwastam bai wuce mintuna 30 ba, da kuma kara tuntuba tsakanin hukumomi masu ruwa da tsaki da kwastam, don tabbatar da gudanar da ayyukan kwastam cikin hanzari ba tare da samun matsala ba. (Amina Xu)