Tun daga ranar Asabar, wato ranar jajiberin sabuwar shekarar Sinawa bisa kalandar gargajiya ta wata ta kasar, daruruwan miliyoyin Sinawa sun fara shagulgulan bikin bazara, ko bikin sabuwar shekarar kasar, bikin da shi ne mafi girma ga al’ummar kasar ta Sin.
Bukukuwan da a shekarun baya bayan nan aka saukaka su sakamakon annobar COVID-19, a bana suna gudana yadda ya kamata, bayan da gwamnatin kasar ta yi umarnin sassauta matakan yaki da annobar ta COVID-19, tun daga farkon watan nan na Janairu.
Mako guda da za a shafe ana hutu da shagulgulan bikin a bana, na nuna cewa al’amura sun fara komawa kamar yadda aka saba a kasar. Alkaluman hukuma sun nuna cewa, a bana, tafiye tafiye yayin bikin bazara, ko “chunyun,” da yaren Sinanci, sun doshi biliyan 2.1, adadin da ya kusa ninka wanda aka samu a shekarar 2022 da ta gabata.
Bisa alkaluman, sama da rabin tafiye tafiyen da ake yi ta hanyoyin mota, da jiragen kasa da na sama, ana yin su ne domin zuwa ganin gida da haduwa da iyalai, yayin da wasu da dama ke ziyartar wuraren bude ido na cikin gida da na waje. (Saminu Alhassan)