Masana sun yi ittifakin cewa, albasa na da wasu muhimmman sinadarai da ke taimakawa wajen gina jikin Dan’adam; baya ga wasu sinadaran da ta ke kunshe da su, masu matukar tasiri kan wasu cututtukan jiki.
Babu shakka, al’umma sun jima suna amfani da albasa; don magance cututtukan da ke damun su, kamar ciwon sanyin kashi, mura, ciwon makogoro, gabobi da sauran makamantansu.
Maganin Tari, Mura Ko Ciwon Makogoro
Albasa na maganin sanyi, mura ko ciwon makogoro; duk wanda ke fama da daya daga cikin wadannan cututtuka, sai ya nemi man Albasa cikin babban cokali guda tara da zuma babban cokali shi ma tara, sai ya zuba man albasar cikin zumar ya gauraya su sosai, daga nan sai ya samu mazubinsa mai tsafta; kuma mai murfi ya adana ya a rika shan cokali uku a kullum, safe da rana da kuma dare.
Maganin Zafin Fitsari.
Ana amfani da albasa, don magance matsalar fitar fitsari da zafi, musamman ga mutumin da ke shan wahala wajen fitar fitsari; ya nemi man albasa ya hada da zuma mai kyau da lemon tsami ya gauraya su tare, ya kuma tabbatar sun gaurayu sosai, sai ya rika sha sau biyu a rana, ma’ana safe da yamma, sannan kuma ya rika shafa man albasar ajikin mararsa.
Maganin Sanyin Kashi
Albasa na maganin sanyin kashi. Don haka, duk mai fama da wannan matsala, sai ya nemi albasa ya dafa ta, ya zuba man zaitun a rika dumama wajen da yake jin ciwon, sannan da dare kafin ya kwanta barci; sai ya shafe wajen ciwon da wannan hadin, sannan kuma ya rika sha da safe; har tsawon kwana bakwai.
Maganin Maruru Ko Kuraje
A nan, albasa za a samu a kirba ta; a hada da man zaitun a dafa, a rika wanke marurun ko kurajen, bayan an gama wankewa; sai a shafa man zaitun a wurin.
Maganin Zubar Gashi
Duk matar da ke fama da zubewar gashi, ta samu ruwan albasa; ta hada da man Simsim da garin Bakadunas Simsim da kuma garin Bakadunas, ta rika shafe kanta da shi; ta tabbatar ta game kanta tun daga matsirar gashinta. Haka za ta rika yi kullum kafin ta kwanta barci, bayan gari ya waye; sai ta wanke kan nata da ruwan dumi har tsawo mako guda.
Maganin Lagwada
Ga duk mai fama da wannan matsala ta ciwon lagwada, sai ya samu ruwan albasa ya hada da ruwan Kahl a zuba a wajen a daure, sai bayan kwana daya ko biyu; sai a kwance idan ba ta cire ba, sai a sake maimaitawa har sai ta cire.
Maganin Karfin Mazakuta
Guda daga cikin amfanin albasa ga lafiyar Dan’adam, akwai maganin karfin maza. Ga mai son amfana da wannan fa’ida ta albasa, sai ya samu kofi daya na ruwan zuma mai kyau, marar hadi da rabin kofi na ruwan albasa, ya zuba cikin tukunya ya dora a kan wuta; idan ya fara tururi, sai ya sauke ya rika shan babban cokali daya sau uku a kullum.
Maganin Amosanin Kai
Duk wanda ke fama da amosanin kai, ya samu ruwan albasa ya hada da man Simsim da kuma garin Bakadunas; ya rika shafa wa a kansa, ya kuma tabbatar ya game kan nasa tun daga matsirar gashi. Haka, zai rika yi kullum kafin ya kwanta barci. Idan gari ya waye, sai ya wanke da ruwan dumi; har tsawon mako guda.
Maganin Daji (Cancer) Na Fata
Ana amfani da albasa wajen maganin ciwon dajin fata. Idan mutum yana fama da wannan matsala, sai ya samu ruwan albasa da garin hulba da kuma karamin cokali na farar wuta. Daga nan, sai y hada ruwan albasar da garin hulba da kuma farar wutar waje guda ya gauraya su, ya rika shafawa a kan ciwon safe da yamma; har tsawon tsawon mako biyu.
Albasa Na Taimaka Wa Masu Ciwon Sikila
Daga cikin irin amfanin albasa ga lafiyar Dan’adam, akwai taimaka wa masu fama da cutar sikila. Idan mutum na fama da wannan matsala ta sikila, sai ya rika yanka albasa tare da ganyen Zogale yana ci. In sha Allahu, zai samu saukin ciwon.
Daga taskar ma’aurata