Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.
Ganyen Gwanda yana da matukar amfani sosai a jikin dan’Adam, yana da sinadaran magunguna da dama, mun taba magana akan yana maganin ciwon sanyi, yanzu kuma gashi za mu kawo muku yadda yake gyara gashin mace, idan mace tana amfani da shi ba ruwanta da salon saboda yana gyara gashi, yana sa gashi ya yi kyau ya yi baki da laushi sannan ya yi santsi, sannan yana hana zubar gashi da kakkaryewar gashi.
Yadda ake amfani da shi:
Idan kika samu Ganyen Gwanda sai ki wanke shi ki dan sa masa dan gishiri wajen wankewar, sai ki daka shi ko kuma ki yi ‘bilanding’ din sa sai ki tace ruwan, idan za ki wanke kanki, ruwan za ki sa a kanki wato za ki sa shi kamar shamfo sai ki yi ta murtsikar gashin da shi kamar sabulu sai ki wanke shi, idan kika hakan za ki ga abin mamaki sosai, sai an gwada akan san na kwarai.