7. A bi sannu wurin mayar da hakoran da aka sa su zama farare
Ana samun mutane da daman gaske wadanda ake sa musu hakora da aka kera sakamakon zubewar nasu.
To lallai duk wadda ta ko ya san yana da ire-iren wadannan hakora da yawa a bakinsa, ya bi sannu yayin da yake amfani da sinadaran tsaftace hakora su koma farare.
Kar mutum ya ce dole sai sun yi farare kamar sauran wadanda suka tsiro daga bakinsa, ba za su taba zama daya ba. Saboda haka kar a bari garin neman kiba a samu rama, maimakon a goge hakorin don ya yi fari sai kuma ya t u m b u k e , wanda dole sai an sake ganin likita.
8. Rigakafin daudar hakora
Yayin da girma ke kama mu, hakoranmu su ma suna kara tsufa. Kasan hakoranmu sukan sauya launinsu zuwa rawaya, don haka ake so tun tasowar mutum kafin girma ya kama shi ya kasance mai kokarin tsaftace hakoransa musamman wurin kula da su, su ci gaba da zama farare.
Matukar za a kiyaye da irin mabinci da abin sha masu bata launin hakori sosai, akwai yiwuwar hakora za su kasance tsaf-tsaf da farinsu har kusan tsawon shekara guda. Idan kuma aka matsa wa hakoran da goge-goge da amfani da sinadarin mayar da su farare fiye da kima, a nan ma ana iya samun matsala, don launinsu zai rine ya koma ruwan bula.
Don haka a yi hattara, a kula da su ba tare da matsawa sosai ba.
9. Kaurace wa shan shaye-shayen hayaki
Shaye-shayen abubuwa na hayaki kamar taba sigari ko wiwi da sauransu ba kawai suna da matsala ga lafiyar mutum ba ne, suna kuma daga cikin na sahun gaba wajen bata hakori.
Taba sigari kan sa hakori ya yi baki tare da bata dasashi da sauran sinadaran da ke rike da hakori.
Matukar hayaki ya bata wa mutum hakora yana da matukar wahala a iya kawar da shi ta hanyar goge baki da burushi kawai.
Yawan adadin shan hayakin mutum yawan yadda zai bata masa hakora.
Shaye-shaye mugun abu ne da ke haifar da cuta ga sinadarin da ke rike da hakori a baki tare da haifar da cutar daji, sannan duk mai wannan dabi’a ta shaye-shaye da wahala ya bude baki ba ka ji mugun wari ba.
Saboda haka matukar kana so hakoranka su ci gaba da zama tsaftsaf, ta kaurace wa bushe-bushen hayaki.
10. Abinci ko abinsha mai bata hakori
Wani dalili da ke sa hakora su dushe daga asalinsu shi ne irin abincin da ake ci ko ake sha, kamar dai yadda muka fara kawo bayanin haka a sama.
Akwai wasu nau’o’in abinci masu bata hakora. Hanya mafi sauki da za ka iya gane abinci ko abinsha mai bata hakora ita ce, duk abin da aka zuba shi a farar rigar da aka saka da farin auduga ya bata, to zai bata hakora kamar yadda likitocin hakora ke fada. Misali, shayin gahawa (coffee) zai iya bata hakora.
Sauran abubuwan sha da suke bata hakora sun hada da ganyen shayi, abubuwan sha na soda masu duhu da sauran tatattun lemuna.
A hankali wannan dafewar hakora ke aukuwa yayin da ake amfani da wadannan nau’o’in abincin da abin sha, yayin da girma ke kamawa sai su rika bayyana.
Shi ya sa mafita daya ita ce, duk lokacin da ka yi amfani da wadannan abubuwan, ka yi maza ka tsaftace hakoranka kar daudar ta samu mazauni.
Mu hadua mako na gaba domin ci gaba, mun samo muku daga shafin webmad.com