Rundunar Sojojin Nijeriya da ke yaki da ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yammacin kasar, sun yi nasarar dakile yunkurin yin garkuwa da mutane da dama, tare da kashe dan ta’adda guda daya tare da kubutar da wasu mutane bakwai da aka yi garkuwa da su.
A wata sanarwa da rundunar sojin Nijeriya ta fitar a shafinta na X, ta ce, sojoji a ranar Talata 7 ga Mayu, 2024 yayin da suke aiki da bayanan sirri, sun yi artabu da mayakan ISWAP a kauyen Kulukawiya da ke karamar hukumar Nganzai ta jihar Borno.
- Bincike: Majalisar Kaduna Ta Tattauna Da Tsoffin Kwamishinoni Da Manyan Sakatarori A Gwamnatin el-Rufai
- Gwamnatin Kano Ta Rattaba Hannu Kan Dokar Yin Gwaji Kafin Aure
Bayan artabun, sojojin sun kashe dan ta’adda guda tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, tare da ceto wani yaro da suka yi garkuwa da su.
Sanarwar ta ce, yaron, tuni an hada shi da mahaifinsa, Alhaji Musa.
A wani samame daban da aka yi a jihar Kaduna, sojojin sun amsa kiran gaggawa daga kauyen Agunu Dutse da ke karamar hukumar Kachia yayin da ‘yan ta’addan suka yi wa mazauna unguwar kawanya.
Sojojin da isarsu garin, sun yi nasarar ceto wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su, da suka hada da mata biyu da kananan yara hudu.
An kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da jin rauni ba kuma an hada su da iyalansu.