Dakarun Rundunar Sojin Nijeriya ta 6, sashe na 3 karkashin ‘Operation Whirl Stroke (OPWS)’, sun mamaye dajin Fajul da ke karamar hukumar Ibi a jihar Taraba domin fatattakar ‘yan ta’adda daga maɓoyarsu.
Mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Laftanar Umar Muhammad, ya ce ‘yan ta’addan da aka fatattaka sun kasance suna yi wa mazauna kauyukan Badekoshi, Fajul, Kurmi da Dampar da ke karamar hukumar Ibi barazana da rayuwarsu.
- Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles
- Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
A cewar Muhammad, sojojin sun kuma samu nasarar kwato makamai, kayan sawa da babura, a ci gaba da gudanar da ayyukan sharar daji a karkashin rundunar ‘Operation Lafiya Nakowa’ domin fatattakar ‘yan ta’adda da ‘yan fashi da sauran masu aikata laifuka a jihar Taraba.
Kwamandan rundunar ta 6, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yabawa sojojin bisa nuna kwarewa da juriya, inda ya bukace su da su ci gaba da sharar daji har sai an kakkaɓe duk wasu masu aikata laifuka gaba daya a jihar Taraba.
Ya bayyana ci gaba da jajircewar rundunar sojin Nijeriya wajen tabbatar da tsaro da tsaron duk ‘yan kasa masu bin doka da oda, yana mai ba da tabbacin cewa, sojojin za su ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro da al’ummomin yankin domin samun dawwamammen zaman lafiya a jihar.