Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kama wani fitaccen jagoran masu aikata laifuka wanda ake nema ruwa a jallo mai suna Idris Idris (Babawo Badoo), tare da wasu mutane 37 da ake zargi da aikata laifuka.
Rundunar sojin Nijeriya a cikin wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na sada zumunta a ranar Alhamis, ta kuma ce sojojinta a yayin gudanar da aikin hadin gwiwa a fadin kasar sun ceto mutane 15 da aka yi garkuwa da su, tare da kashe ‘yan ta’adda biyu tare da kwato makamai daban-daban, alburusai da kayayyaki.
Sanarwar ta ce, babban wanda ake zargin, Babawo Badoo, an kama shi ne a ranar 20 ga watan Oktoba, 2025, ta hannun dakarun Operation ‘ENDURING PEACE’ a kauyen Lugere da ke karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato.
Sanarwar ta ce, sojojin sun yi aiki da sahihan bayanan sirri, sun kama wanda ake zargin tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, da wata mujalla cike da harsashai na musamman masu tsawon 7.62mm har guda 10, wayar hannu, da kuma kudi naira 12,000.
“Sakamakon nasarar da aka samu ya haifar da babbar illa ga kungiyar masu tada zaune tsaye da ke aiki a yankin Arewa ta Tsakiya,” in ji sanarwar