Dakarun sojin Nijeriya da ke aiki a Malekachi a dajin Sangeko a karamar hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi, sun yi nasarar kashe wani kwamandan ‘yan bindiga mai suna ‘Mainasara’.
Wasu ‘yan bindiga biyu da ake kyautata zaton suna daga cikin gungun ‘yan fashin mai suna Mainasara da ke kai munanan hare-hare da garkuwa da mutane a yankunan da sojoji suka yi nasarar kashe su.
- An Yi Waje Rod Da Arsenal A Gasar Carabao Cup
- Dankwambo Ya Ce Daga Yanzu Gwamnatin Gombe Ta Daina Biyansa Fansho Ya Yafe
Daraktan tsaro na ofishin majalisar zartarwa na Birnin Kebbi, AbdulRahman Usman ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a Birnin Kebbi.
Ya kara da cewa, “A yayin da sojojin ke sintiri na yau da kullum a dajin Sengeko da misalin karfe 07:30 na safe, kwatsam sai suka yi artabu da ‘yan bindigar.
“A yayin musayar wuta, ‘yan bindigar sun yi kokarin tserewa amma sojoji sun kashe su sannan kuma an kwato baburan hawa guda biyu tare da lalata su kafin sojojin su koma FOB Malekachi,” in ji shi.
Daraktan Tsaro ya kara da cewa nasarorin da jami’an tsaro suka samu a jihar sun biyo bayan yunkurin da Gwamna Nasir Idris ya dauka ne, saboda irin goyon bayan da yake bai wa jami’an tsaro da ke aiki a jihar ba tare da gajiyawa ba.