Dakarun runduna ta daya ta sojojin Nijeriya da ke Kaduna, a ci gaba da kokarin kawar da ‘yan ta’adda, sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda daga maboya da dama, inda suka kashe 14 daga cikinsu, tare da samun nasarar kwato manyan makamai da sauran kayayyaki a wasu hare-haren hadin gwiwa a jihohin Kaduna da Neja.
A cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya, Laftanar Kanar Musa Yahaya, ya fitar kuma aka rabawa manema labarai, ta ce a jihar Neja a ranar 23 ga watan Disamba, 2023, sojojin sun kai hare-hare garin Madawaki da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar inda suka kashe wasu mahara biyu sauran suka tsere da raunukan harbin bindiga.
- Adadin Masu Fama Da Cututtukan Numfashi Dake Neman Jinya A Cibiyoyin Lafiya A Kasar Sin Na Raguwa
- Hukuncin Kotu: INEC Ta Baiwa ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Filato 16 Shaidar Lashe Zabe
Ya kara da cewa, sojojin sun kwato bindigogin AK47 guda biyu, kwalbasar alburusan AK47 guda biyu da babur daya.
“Sojoji sun zarce zuwa sansanin da aka kashe jagoran ‘yan bindiga, Ali Kachalla, inda ragowar ‘yan ta’addan suke, yayin da suka hango tawagar jami’an tsaron sai suka tsere suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su a sansaninsu su 13, dukkansu maza ne, an sace su ne a jihar Neja a ranar 13 ga Oktoba 2023,” in ji shi.
Babban kwamandan runduna ta daya ta (GOC) kuma kwamandan rundunar ‘Operation WHIRL PUNCH’ Manjo Janar Valentine Okoro ya bayyana jin dadinsa da nasarorin da aka samu a hare-haren, ya kuma yabawa sojojin bisa wannan kwazon da suka nuna.