Sojoji sun kashe ‘yan bindiga hudu a wani farmaki biyu da suka kai a kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa a jihar Kaduna.
Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana wa manema labarai a Kaduna a ranar Talata 17 ga watan Satumba.
- An Kammala Bikin Baje Kolin CIFTIS Tare Da Nasarori Masu Tarin Yawa
- Ambaliya: Muna Da Bayanan Fursunonin Da Suka Tsere A Maiduguri — Hukuma
Sanarwar ta ce, sojojin na ‘Operation Forest Sanity’ sun fara aikin share fage na musamman ne a yankin Alawa, karamar hukumar Birnin Gwari.
“Rundunar sojojin sun yi wa ‘yan ta’addan kwanton bauna a kusa da kauyen Kwaga, inda suka samu nasarar kashe biyu daga cikinsu sannan sauran suka gudu cikin daji da raunukan harsashi.
Sanarwar ta kara da cewa, sojoji da ke ‘Sector 6 Operation Whirl Punch’ sun kuma gudanar da sintiri a kusa da kauyen Nakwakina, karamar hukumar Giwa. Bayan sahihan bayanan sirri, an ce, sojojin sun yi kwanton bauna a hanyar da ‘yan ta’addan ke bi wajen zuwa sansanonin su.
“bayan arangama da sojojin, an kashe biyu daga cikin ‘yan ta’addan yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
“A wani samamen kuma, dakarun sojoji da ke ‘Sector 3, Operation Whirl Punch’ da ke sintiri a kan titin Kwaga zuwa Folwaya, a karamar hukumar Birnin Gwari, sun amsa kiran gaggawa tare da tarwatsa wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da wasu mutane da ke kusa da kauyen Folwaya.
“Bayan tarwatsa ‘yan bindigar, sojojin nan take suka kubutar da mutanen 20 da aka yi garkuwa da su tare da sake hada su da iyalansu.”
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana farin cikinsa da duk rahoton da aka bayar, ya kuma godewa jami’an tsaron kan namijin kokarin da suke yi na tsare dukiyoyi da rayukan al’umma.