Dakarun rundunar ‘Operation Forest Sanity’ sun kashe ‘yan bindiga da dama tare da kubutar da wasu mutane 10 da aka yi garkuwa da su sannan aka daure su da sarka a wani sansani a kananan hukumomin Chikun da Igabi a jihar Kaduna.
An bayyana cewa sojojin sun share sansanoni a tsaunin Apewohe, Dakwala da Kunai a karamar hukumar Chikun.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da kuma harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an sake share wani sansani da ke ‘Daban Lawal Kwalba’ a karamar hukumar Igabi.
“Sojojin bayan sun fatattaki ‘yan bindigar sun ceto mutane 10 da aka yi garkuwa da su sannan aka daure su da sarka.” inji shi
Ya ce gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufa’i, ya yaba wa dakarun da suka gudanar da aikin tare da karfafa musu gwiwa da su ci gaba da ragargazar ‘yan ta’adda ba kakkautawa.