Dakarun Sashe na 2 tare da hadin gwiwar Rundunar Sojojin Sama na Operation Fansan Yamma sun kashe ‘yan ta’adda 10 tare da kubutar da wasu 101 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Zamfara.
An samu wannan nasarar ne a wani farmakin da aka gudanar a tsakanin ranakun 17 zuwa 18 ga watan Maris, wanda ya kai ga kashe ‘yan ta’adda 10 a gundumar Faru da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi Akwa ya fitar, ya ce, sojojin sun kum kaddamar da wani farmaki kan wata maboyar ‘yan ta’adda a tsaunin Pauwa da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp