A ci gaba da aikin fatattakar ‘yan ta’adda da rundunar sojin Nijeriya ke yi a Kaduna, ta ci gaba da samun nasara inda ta kashe ‘yan ta’adda 10 cikin mako guda tare da kwato makamai daga hannun ‘yan ta’addan.
A cewar wata sanarwa da mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya, Laftanar Kanar Musa Yahaya ya fitar, ya ce, bayan wani samame da dakarun runduna ta daya da rundunar Operation Whirl Punch suka kai a yankin Kampanin Doka, a ranar 1 ga Nuwamba, 2023, a kauyen Birnin Gwari na jihar Kaduna, wasu ‘yan bindiga hudu da suka addabi al’ummar yankin sun gamu da ajalinsu.
- Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Sheikh Yusuf Ali
- Yadda Mahara Suka Kashe Mutane Da Sace Wasu Da Dama A Wurin Maulidi A Katsina
A yayin samamen, sojojin sun kwato bindiga kirar AK47 guda daya, kwalbasar harsashin AK47 daya da babura 14 da sauran kayayyaki daga hannun ’yan ta’addan.
A wani labarin makamancin haka, a samamen da rundunar ke kaiwa a yankunan Birnin Gwari ta jihar Kaduna, sojin sun samu nasarar kashe ‘yan bindigar har shida da kwato makamai a samame daban-daban.
Babban kwamandan runduna ta daya ta Nijeriya (GOC) wanda ke rike da mukamin kwamandan runduna ta Operation Whirl Punch, Manjo Janar VU Okoro, ya yabawa sojojin bisa jajircewar da suka yi, ya kuma umurce su da su ci gaba da kai samame har sai duk ‘yan ta’adda da masu aikata muggan laifuka a Yankin sun hadu da ajalinsu.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Kaduna da su ci gaba da baiwa sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro bayanan tsaro masu inganci da za su taimaka wajen gano ayyukan ‘yan ta’addan da sauran masu aikata miyagun laifuka.