Hedikwatar Hukumar Tsaro ta kasa (DHQ) a ranar Alhamis ta ce, dakarun sojoji da aka tura aiki sassan kasar nan, sun samu nasarar hallaka ‘yan ta’adda 151 tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su 76, kuma sun cafko ‘yan ta’adda 456 a sameme daban-daban da suka aiwatar a cikin mako guda tak.
Daraktan sashin yada labarai na hukumar tsaron, Manjo Janar Edward Buba, shi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke ganawa da manema labarai kan ayyukan da sojojin suka aiwatar, inda ya ce, wasu mutum 45 da ake zargin barayin Danyen Man fetur ne, su ma an kamasu yayin da kuma aka kwato mai da darajarsa ya kai Naira Biliyan N1,011,851,250 da suka sace.
Ya ce, sojojin sun kuma kwato makamai daban-daban har guda 216 da alburusai 443.
Da yake jero makamai da kayayyakin da sojojin suka kwato, Buba ya ce, an kwato bindiga kirar AK47 guda 62, bindiga mai amon harsasai guda 7, harbi ka noke guda 19, fistol guda 3, wasu bindiga kirar gida guda 10, fistol kirar gida 5, nakiya (IED) guda 399, harsasai masu rai samfurin 7.62mm special ammo guda 225, alburusai samfurin 7.62mm NATO guda 10, alburusai samfurin 9mm ammo guda 13, harsasai 7.62mm x 54mm guda 20, harsasai samfurin cartridges guda 57, 49 magazines, motoci 21, machine hudu, keke-napep daya, wayoyin salula ukulele, da kudi da yawansu ya kai N3,194,450.00.
Kazalika, sojojin da ke aiki a yankin Neja-Delta sun gano gami da tarwatsa gidajen karkashin kasa guda 21, jiragen ruwa 56, tukwanan adana abinci 138, nau’in abun dumama abinci (oven) guda 235, injunan ban ruwa 6, wasu jirgin ruwa guda 2 masu gudun tsiya, haramtatun wuraren tace mai 89 da kudi naira N13,950.
Sannan kuma sojojin sun kamo litar danyen mai 1,205,950 da aka sace, litar gas 452,910, litar man fetur guda 22,650 da kuma litar kananzir 3,000.
Ya ce, sojoji ba za su daina kokarin da su ke yi ba na dakile aniyar bata gari da ‘yan ta’adda ba.