A kalla ‘yan ta’adda 181 ne aka kashe sannan aka cafke wasu 203 da ake zargi, ciki har da wani dan bindiga mai suna Mohammed Musa (Mamman) da sojojin Nijeriya suka kama a cikin mako guda da ya gabata.
Hedikwatar tsaro (DHQ) ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya fitar ranar Juma’a.
- Xi Ya Gabatar Da Muhimmin Jawabi A Babban Taron Ayyukan Tattalin Arziki Na Tsakiya
- Shugaban NPA Ya Kai Ziyarar Neman Masu Zuba Jari A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Onne Da Ta Jihar Ribas
Manjo janar Buba ya kara da cewa, sojojin sun kuma kubutar da mutane 161 da aka yi garkuwa da su tare da kama wasu mutane 50 da ake zargin barayin mai ne tare da kwato man da aka sace wanda kudinshi ya kai Naira miliyan 728,297,650.00.
Kakakin tsaron ya ce, sojojin sun kuma kwato makamai iri-iri 228 da alburusai 6,749 duk a cikin mako guda.