Akalla ‘yan ta’adda 481 ne aka kashe, an kuma kama wasu 741, yayin da sojojin Nijeriya kuma suka kubutar da mutane 492 da aka yi garkuwa da su a cikin watan Oktoba, kamar yadda hedikwatar tsaro ta bayyana a ranar Alhamis.
Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya kuma bayyana cewa, sojojin sun kwato makamai 480 da alburusai iri-iri 9,026.
- Makinde Ya Amince Da N80,000 A Matsayin Mafi Karancin Albashin Ma’aikata
- Gwamnan Zamfara Ya Yi Gargaɗi Kan Yanke Wa Ma’aikata Kuɗi Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Maj.-Gen. Buba ya ci gaba da cewa, ‘yan ta’addan ba za su iya kwatanta karfinsu da na soji ba, don haka, ya shawarce su da su ajiye makamansu su mika wuya ga sojoji ko kuma su kasance cikin shirin fuskantar fushin sojoji.
Janar Buba ya sake nanata cewa, sojoji za su ci gaba da aiki tukuru domin kashe ‘yan ta’adda, da dakile rashin tsaro a cikin al’umma da kuma tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan kasa.
Ya kara da cewa, sojojin na ci gaba da kasancewa a matsayi mai kyau da karfi domin samun nasara a yakin da suke da ta’addanci.