Dakarun rundunar ‘Operation Hadin Kai’ (OPHK) da sanyin safiyar Talata 27 ga watan Mayun 2025, sun dakile wani hari da ‘yan ta’addar Boko Haram/ISWAP suka kai musu a garin Marte na jihar Borno.
A wata sanarwa da mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar OPHK, Kyaftin Reuben Kovangiva, ya fitar, ya ce an dakile harin ne da gamayyar hadin gwiwar sojojin kasa da kuma na sama na OPHK.
- Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Amso Bashin $21.5bn Da ₦757.9bn
- Tsarin Dunkulewar Aiki Ba Da Ilmi Da Kimiyya Da Kwararru Na Sin Ya Dace Da Yanayin Zamani
Kyaftin Kovangiva ya ce, an kawar da da dama daga cikin maharan yayin da sojoji biyu suka rasu a fafatawar.
A cewar Mukaddashin Daraktan, ‘yan ta’addar sun yi yunkurin kutsawa inda sojojin suke, amma suka gamu da karfin soji.
Ya kara da cewa, Rundunar Sojan Sama ta bayar da bayanan sirri tare da karfafawa sojin kasa, wanda ya kai ga halaka sauran ‘yan ta’addan da suka tsere.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp