Akalla mutane 386 wanda mafi yawancinsu mata da kananan yara ne da Sojoji suka ceto a dajin Sambisa shekaru goma bayan garkuwa da su.
Mukaddashin shugaban runduna ta 7 (GOC 7 Division), Birgediya Janar AGL Haruna, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen dajin Sambisa a karamar hukumar Konduga bayan ya karbi bakuncin sojojin da suka ceto mutanen bayan gudanar da hare-hare na kwanaki 10 a dajin.
- Mataimakin Shugaban Kasa Ya Buɗe Sabon Gidan Gwamnatin Bauchi
- Zulum Ya Bukaci Sojojin Nijeriya Da Su Kafa Sansani A Dajin Sambisa
Haruna ya bayyana cewa, aikin wanda aka yi wa take da “Operation Desert Sanity 111”, an yi shi ne da nufin kakkabe Dajin Sambisa daga sauran ragowar nau’ikan ‘yan ta’adda a dajin tare da bude kofa ga masu sha’awar mika wuya kamar yadda aka samu a baya.
“Kokarin da muke yi shi ne, mu tabbatar da cewa mun kawar da ragowar ‘yan ta’adda a Sambisa tare da bai wa masu son mika wuya dama.
“Da wannan nasarar, muna sa ran da yawa daga cikinsu za su mika wuya kamar yadda suka fara.
“Mun kuma ceto mutane da yawancinsu mata da kananan yara ne su 386 kuma na tabbatar za a ci gaba da ceto sauran” inji Birgediya Janar Haruna.