Rundunar sojin Nijeriya, bayan wani samame da ta samu nasarar gudanarwa a dajin Gundumi da ke Sokoto, ta mika wasu mutane 66 da ta ceto daga hannun ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ga gwamnatin jihar Sokoto a ranar Lahadi.
Kwamandan runduna ta 8, Birgediya Janar Amos Tawasimi, a lokacin da yake mika mutanen ga gwamnatin jihar, ya ce an ceto 52 a ranar Juma’a, yayin da wasu 14 kuma aka ceto su a ranar Asabar.
- An Yi Hasashen Kone Gas Na Girki Na Naira Tiriliyan 1.5 A Nijeriya Badi
- Dalilan Da Suka Jawo Hankalin ‘Yan Kasuwan Ketare Zuwa Sin Kafa Kamfanoni
Ya yabawa gwamnan bisa goyon bayan da yake baiwa jami’an tsaro tare da tabbatar da cewa rundunarsa za su ci gaba da fatattakar ‘yan ta’addan.
Da yake jawabi yayin karbar wadanda aka ceton, gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya yabawa rundunar sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro a jihar bisa kokarinsu da jajircewarsu wajen yaki da ‘yan ta’adda a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp