Kasar Madagaska ta koma karkashin mulkin soji a yau Laraba bayan da wasu manyan sojojin kasar suka kwace mulki bayan tsige shugaban kasar, Andry Rajoelina, tare da yin alkawarin gudanar da zabe cikin shekaru biyu.
Wannan dai shi ne na baya bayan nan da wata kasar da Faransa ta yi wa mulkin mallaka ta fada karkashin mulkin soja tun shekarar 2020, inda aka yi juyin mulki a Mali, Burkina Faso, Nijar, Gabon, da Guinea.
Kwamandan rundunar sojin ta CAPSAT Kanar Michael Randrianirina, wanda kotun kasar ta amince ya jagoranci kasar, ya ce, zai mika mulki ga farar hula nan da tsawon shekaru biyu kuma zai tabbatar an yi kwaskwarima da sake fasalin manyan cibiyoyin gwamnatin kasar.














