Dangane da kalaman da jami’an Amurka suka yi kan zargin kasar Sin cewa, wai jiragen ruwa da na saman Sin da yin katsalanda, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Talatar nan cewa, gaskiyar magana ita ce, jiragen ruwa da na saman sojan Amurka sun yi tafiyar dubban milamilai don tada hargitsi a kasar Sin.
Wang Wenbin ya ce, jiragen ruwa da na saman Amurka sun dage kan yin aikin leken asiri a kusa da yankunan ruwa da sararin samaniyar kasar Sin, domin nuna karfinsu. Wannan ba batu ne na kiyaye ‘yancin yin zirga-zirga ba ne, a’a, amma don inganta “ikon zirga-zirga”, wanda ke ba da damar yin tsokanar soja ce karara, wannan ta’addancin da ake yi shi ne ginshikin matsalar tsaro a yankin teku da sararin samaniya.
Wang Wenbin ya jaddada cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana mutunta ‘yancin yin zirga-zirga da jiragen saman kasashe ke amfani da su, kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada, amma tana adawa matuka da sanya ‘yancin mulkin kai da tsaron kasar Sin cikin hadari da sunan ‘yancin yin zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa. (Mai fassarawa: Ibrahim)