• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojojin Chadi Sun Fatattaki ‘Yan Boko Haram Zuwa Kamaru Da Nijar Da Nijeriya

byRabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
11 months ago
Chadi

Gwamnatin kasar Chadi ta fada cewa daruruwan mayakan Boko Haram na ficewa daga yankin tsakiyar Afirka suna tsallakawa zuwa kasashen Kamaru da Nijar da kuma Nijeriya.

Gidan talabijin din kasar ya rawaito mayakan sun tsere bayan arangama da sojojin Chadi a karshen mako, wanda ya yi sanadin kashe mayakan Boko Haram sama da 100 da kuma sojojin Chadi kusan 20.

  • Boko Haram Ta Hallaka Sojoji 40 A Chadi
  • MOFA: Kasar Sin Na Son Sanya Sabon Kuzari A Ci Gaban Tattalin Arzikin Yankin Asiya Da Tekun Fasifik Da Ma Duniya

Tashar talabijin ta kasar Chadi ta bayar da rahoton cewa, ana ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin ‘yan Boko Haram, inda sojojin suka sami asarar rayukan kusan sojoji 20, tare da jikkata wasu 32 a wani artabu da suka yi da ‘yan ta’addar Boko Haram a yankin tafkin Chadi a ranar Asabar.

LABARAI MASU NASABA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta ce kimanin mayakan Boko Haram 100 ne suka mutu, yayin da wasu 100 suka samu raunuka, inda mayakan na Boko Haram ke tserewa zuwa kasashen Kamaru da Nijeriya da kuma Nijar.

A farkon watan nan ne sojojin kasar Chadi suka kaddamar da wani farmaki da nufin fatattakar ‘yan ta’addar Boko Haram daga yankunan da ke kusa da tafkin Chadi, a cewar shugaban kasa, Janar Mahamat Idriss Deby.

Deby ya ce farmakin mai suna Haskanite, na zama a matsayin daukar fansar kashe sojojin gwamnati 40 a watan Oktoba, da kuma inganta tsaro ga fararen hula a yankin.

Hare-haren ya haifar da ‘da mai ido a makon da ya gabata, lokacin da Deby ya ce sojojin Kamaru da Nijeriya da kuma Nijar, wadanda dukkansu ke ba da gudummawar sojoji ga rundunar hadin gwiwa ta yaki da ta’addanci a yankin, sun yanke shawarar kin hada kai da harin na Chadi.

Kasashen Kamaru da Nijeriya da Nijar ba su bayar da wata sanarwa a bainar jama’a ba, da ke tabbatarwa ko musanta ikirarin na Deby ba, kuma Muryar Amurka ba ta iya tabbatarwa da kanta ba, ko kasashen uku sun zabi kin shiga aikin na Chadi.

Sojojin Kamaru sun ce tsaro ne kan iyakokin kasar da kuma kare fararen hula.

Deby ya ce ya shirya janye sojojinsa daga rundunar kasa da kasa da ke da kusan dakaru 11,000, saboda rashin samun abin da ya kira hadin kai tsakanin kasashe mambobin kungiyar na yaki da ta’addancin Boko Haram.

Chadi ba ta bayyana lokacin da za ta janye sojojinta daga rundunar hadin gwiwa da ke samun taimakon Majalisar Dinkin Duniya ba.

A shekara ta 2009 ne kungiyar Boko Haram ta kaddamar da tawaye da makamai ga gwamnatin Nijeriya, domin kafa Daular Musulunci. Tun daga lokacin yakin ya bazu zuwa kasashe makwabta kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 40,000 tare da raba sama da miliyan 3 da muhallansu a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu
Siyasa

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Next Post
CMG Da El Comercio Group Na Kasar Peru Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zurfafa Hadin Gwiwa

CMG Da El Comercio Group Na Kasar Peru Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zurfafa Hadin Gwiwa

LABARAI MASU NASABA

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version