LSashen rundunar sojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin (PLA) na yankin kudancin kasar, ya shirya wani atisayen jiragen ruwan soji domin gudanar da sintirin shirin ko-ta-kwana a yankin tekun kudancin Sin.
Wata sanarwa da rundunar ta kudanci ta fitar, ta ce an gudanar da sintirin ne kamar dai yadda ake tsara atisayen soji a kowacce shekara.
Ta kara da cewa, sintirin na shirin ko-ta-kwana na da nufin inganta karfin rundunar na yaki domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalin yankin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp