Rundunonin sojin kasar Sin na sama da na ruwa, sun gudanar da wani sintirin hadin gwiwa na shirin ko ta kwana, a tekun kudancin kasar a ranakun Juma’a da Asabar, a wani mataki na wanzar da zaman lafiya da daidaito a yankin, kamar dai yadda wata sanarwa daga rundunar sojin kasar sashen kudanci ta tabbatar.
Sanarwar ta kara da cewa, rundunar ce ke da alhakin shawo kan duk wasu ayyukan soji, da ka iya haifar da tashin hankali a yankin tekun kudancin kasar Sin. (Saminu Alhassan)