A yau Lahadi ƙasar Spain ta lallasa Ingila da ci 2-1, inda ta lashe kofin gasar cin kofin nahiyar Turai na 2024 da aka kammala a ƙasar Jamus.
An kammala mintuna 45 na farko na wasan babu ci, sai dai La Roja ta fara cin ƙwallon bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, inda Nico Williams ya zura kwallon da Lamine Yamal ya ba shi a minti na 47.
- Kasar Ingila Ta Tsallaka Zuwa Matakin Semi Final A Gasar EURO Ta 2024
- Ingila Da Spain Wa Zai Yi Nasara A Berlin?
A minti na 73 zakunan na ƙasar Ingila suka farke kwallon da aka jefa masu ta hannun Cole Palmer, bayan ɗan wasan tsakiyar Real Madrid Jude Bellingham ya ba shi ƙwallo mai kyau, a mintunan ƙarshe Mikel Oyarzabal wanda ya maye gurbin Albaro Morata ya raba gardama.
Sakamakon ƙarshe na wasan na nufin Ingila ta yi rashin nasara a wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Turai sau biyu a jere bayan ta sha kashi a hannun ƙasar Italiya shekaru biyu da suka gabata.