Djed Spence, ɗan wasan baya na Tottenham, na iya zama Musulmi na farko da zai wakilci babbar tawagar ƙwallon ƙafa ta Ingila.
Kocin Ingila, Thomas Tuchel, ya kira Spence cikin jerin ’yan wasa da za su fafata a wasannin da Ingila za ta yi da Andorra da Serbia a wannan watan Satumba.
- Gwamna Sule Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Fara Yaƙin Neman Zaɓe A Nasarawa
- Tinubu Ya Fara Hutun Aiki Na Kwanaki 10 A Faransa Da Birtaniya
Spence, mai shekaru 25, ya ce ya yi matuƙar mamaki da jin cewa shi ne zai iya kafa wannan tarihi.
Ya ce: “Abin mamaki ne sosai, amma na yadda Allah ne ke yin komai. Ina yi masa godiya koyaushe.”
Lokacin da aka tambaye shi ko ya taɓa tunanin zai buga wa babbar tawagar Ingila wasa bayan ya taɓa wakiltar ƙasar a matakin ’yan ƙasa da shekaru 21, sai ya ce bai taɓa tunanin hakan ba.
Spence ya ƙara da cewa: “Abu na farko, Allah ne mafi girma. Ina yin addu’a sosai, kuma ina gode wa Allah a duk lokacin da nake samun nasara ko lokacin da nake cikin ƙunci, saboda koyaushe yana tare da ni.”
Tottenham ta ɗauki Spence daga Middlesbrough kan yarjejeniyar da ta kai kusan Yuro miliyan 20, amma tsohon kocin ƙungiyar, Antonio Conte, ya tura shi aro zuwa Rennes, Leeds da kuma Genoa kafin dawowarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp