Hamshakin dan kasuwa na Birtaniya Stephen Perry, ya ce tun bayan da Sin ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya ko BRI, kasar ta shige gaba wajen kira ga kasashen duniya da su bunkasa hadin gwiwa, da yin watsi da rarrabuwar kai, da kare moriyar kashin kai kadai.
Mista Perry, wanda ke jagorantar kungiya mai zaman kan ta mai suna “48 Group Club”, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cikin wata rubutacciyar tattaunawa cewa, Sin na kokarin samar da daidaito a batun rikicin Ukraine da na Gaza. Kaza lika Sin ba ta tsoma hannu cikin wadannan tashe tashen hankula, maimakon haka tana iyakacin kokari wajen samar da kyakkyawan yanayi na wanzar da zaman lafiya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp