A ranar Juma’a ne ake sa ran rukunin farko na ‘yan Nijeriya da gwamnatin tarayya ta kwaso daga Sudan da ke fama da yakin basasa za su iso gida.
A wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Alhamis, Abike Dabiri-Erewa, Shugabar Hukumar ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM), ta bayyana cewa 13 daga cikin 40 da aka dauka haya don jigilar ‘yan Nijeriya daga Sudan sun tashi ne tun daga ranar Laraba, inda suka bi ta kan iyaka daga garin Aswan na kasar Masar inda duka ma’aikatan ofishin jakadancin da ke Masar da kuma babban daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) za su tarbi mutanen.
Ta bayyana cewa an bai wa yara da mata fifiko.
Ta kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa duk wadanda ke kasar za a kwaso su.
“Jirgin Boeing 777 daga Airpeace zai tashi daga Legas da yammacin ranar Alhamis kuma zai yi jigilar rukunin farko zuwa gida a ranar Juma’a,” in ji ta.
Dabiri-Erewa a baya ta ce an shawo kan matsalar ‘yan gudun hijirar da ke kan hanyarsu ta zuwa Masar kamar yadda aka gani a wani faifan bidiyo.
Ta ce baya ga dimbin daliban Amurkawa ‘yan Nijeriya da ke kasar Sudan, akwai miliyoyin ‘yan Nijeriya a kasar da ke gudanar da kasuwancinsu na halal kuma suna zaune a can cikin kwanciyar hankali.