Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya musanta cewa, jami’an tsaro sun kama shi kan kalamansa kan halin da kasa ke ciki da kuma sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ya fadi hakan ne a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X (twitter) a ranar Laraba, inda ya ce, “Labarin karya ne kawai da ake dora min”.
- Gwamna Yusuf Ya Gargaɗi Kwamishinoninsa Kan Duk Wani Yunƙurin Kawo Rarrabuwar Kai A Majalisar Zartarwar Kano
- Akwai Buƙatar MDD Ta Shigo Don Binciko Masu Ɗaukar Nauyin Ta’addanci A Nijeriya Daga Ƙetare
Mai taimaka wa Obi kan harkokin yada labarai, Valentine Obienyem, ya musanta rahotannin da ke cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama Obi tare da Margaret, matarsa.
“An sanar da ni labarin karya da ake yadawa game da kama ni. Bari in bayyana a fili, duk wannan ikirarin karya ce. A halin yanzu ina gidana a Onitsha, Jihar Anambra.
“Ku tuna a shekarar da ta gabata a watan Satumba, lokacin da nake kasar Ruwanda, an yi irin wannan karairayi cewa, DSS ta mamaye gidana; yanzu, lokacin da nake gidana a Onitsha, Jihar Anambra, sun ce an kama ni a Abuja.” In ji Obi